Littafi Mai Tsarki

Ayu 42:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji ya sa wa wannan zamani na Ayuba albarka, har fiye da na farko. An ba shi tumaki dubu goma sha huɗu (14,000), da raƙuma dubu shida (6,000), da takarkari dubu biyu (2,000), da jakai mata dubu ɗaya (1,000).

13. Ya kuma haifi 'ya'ya maza bakwai, mata uku.

14. Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya,da ta ukun Keren-Haffuk.

15. Duk ƙasar ba 'yan mata kyawawa kamar 'ya'yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu maza.

16. Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba'in bayan wannan, ya ga 'ya'yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.