26. Ko an sare shi da takobi,Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi,Ba sa yi masa kome.
27. Kamar ciyawa baƙin ƙarfe yake a gare shi,Tagulla ma kamar ruɓaɓɓen itace take.
28. Kibiya ba za ta sa ya gudu ba,Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.
29. A gare shi kulake kamar tushiyoyi ne,Kwaranniyar karugga takan ba shi dariya.
30. Kaifin ƙamborin cikinsa kamar tsingaro ne.Yana jan ciki a cikin laka kamar lular ƙarfe.
31. Yakansa zurfafa su tafasa kamar tukunya,Teku kuwa kamar kwalabar man shafawarsa.
32. Idan yana wucewa sai a ga hasken dārewar ruwa,Yakansa zurfafa su yi kumfa.
33. A duniya ba kamarsa,Taliki ne wanda ba shi da tsoro.
34. Yakan dubi kowane abu da yake mai alfarma,Shi sarki ne a bisa dukan masu girmankai.”