Littafi Mai Tsarki

Ayu 41:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse,Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.

25. Sa'ad da ya miƙe tsaye, ƙarfafa sukan tsorata,Su yi ta tutturmushe juna.

26. Ko an sare shi da takobi,Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi,Ba sa yi masa kome.

27. Kamar ciyawa baƙin ƙarfe yake a gare shi,Tagulla ma kamar ruɓaɓɓen itace take.

28. Kibiya ba za ta sa ya gudu ba,Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.

29. A gare shi kulake kamar tushiyoyi ne,Kwaranniyar karugga takan ba shi dariya.

30. Kaifin ƙamborin cikinsa kamar tsingaro ne.Yana jan ciki a cikin laka kamar lular ƙarfe.

31. Yakansa zurfafa su tafasa kamar tukunya,Teku kuwa kamar kwalabar man shafawarsa.