Littafi Mai Tsarki

Ayu 40:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kai kanka za ka sa mini laifi?Za ka kā da ni don kai ka barata?

9. Kana da ƙarfi kamar na Allah?Kana iya tsawa da murya kamar tasa?

10. “Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka,Ka yafa daraja da maƙami.

11. Ka kwararar da rigyawar fushinka,Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.

12. Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi,Ka tattake mugaye a inda suke.

13. Dukansu ka binne su a ƙasa,Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.

14. Sa'an nan ni kaina kuma zan sanar da kai,Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.

15. “Ga dorina wanda ni na halicce ta,Kamar yadda na halicce ka,Tana cin ciyawa kamar sa.