Littafi Mai Tsarki

Ayu 39:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Gama Allah bai ba ta hikima ba,Bai kuwa ba ta fahimi ba.

18. Amma sa'ad da ta sheƙa a guje,Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.

19. “Kai ka yi wa doki ƙarfinsa?Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza?

20. Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango?Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.

21. Yakan yi nishi a fadama,Yana murna saboda ƙarfinsa,A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.

22. Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba.Ba ya ba da baya ga takobi,

23. Kibau na ta shillo a kansa,Māsu suna ta gilmawa a gabansa.

24. Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa,Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.

25. Sa'ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.

26. “Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi,Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu?

27. Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi samaTa yi sheƙarta can ƙwanƙoli?