Littafi Mai Tsarki

Ayu 39:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa?Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?

2. Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?Ka san lokacin haihuwarsu?

3. Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu,Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu?

4. 'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.

5. “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,

6. Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?

7. Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a,Ba ruwansa da tsawar masu kora.