Littafi Mai Tsarki

Ayu 38:8-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. “Wa ya yi wa teku iyakaSa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?

9. Sa'ad da na suturta ta da gizagizai,Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.

10. Na sa mata iyakoki,Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,

11. Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan,Ba za ki wuce ba.Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’

12. “Ayuba, a dukan kwanakinkaKa taɓa umartar wayewar gari,Ko ka sa alfijir ya keto?

13. Da gari ya waye,Ka kawar da muguntar da ake yi da dare?

14. Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi,Yakan rine kamar riga.

15. Akan hana wa mugaye haske,Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.

16. “Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku?Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku?

17. An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa?Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?

18. Ko ka san iyakar fāɗin duniya?Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.

19. “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?A ina kuma duhu yake?

20. Ka san iyakarsa ko mafarinsa?

21. Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka,Shekarunka kuwa suna da yawa.

22. “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara?Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?

23. Na adana su ne don lokacin wahala,Domin ranar faɗa da ta yaƙi.

24. Ina hanya zuwa inda rana take fitowa,Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko'ina?

25. “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi?Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?