Littafi Mai Tsarki

Ayu 38:18-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ko ka san iyakar fāɗin duniya?Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.

19. “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?A ina kuma duhu yake?

20. Ka san iyakarsa ko mafarinsa?

21. Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka,Shekarunka kuwa suna da yawa.