Littafi Mai Tsarki

Ayu 38:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.

2. “Wane ne wannan da yake ɓāta shawaraDa maganganu marasa ma'ana?

3. Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.

4. A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya?Faɗa mini idan ka sani.

5. Wane ne ya zayyana kusurwoyinta?Hakika ka sani.Wane ne kuma ya auna ta?

6. A kan me aka kafa tushenta?Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?

7. Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare,Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna.

8. “Wa ya yi wa teku iyakaSa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?

9. Sa'ad da na suturta ta da gizagizai,Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.