Littafi Mai Tsarki

Ayu 37:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,Domin dukan mutane su san aikinsa.

8. Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,Su yi zamansu a ciki.

9. Guguwa takan taso daga inda take,Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.

10. Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.

11. Yakan cika girgije mai duhu da ruwa,Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.

12. Sukan yi ta kewayawa ta yadda ya bishe su,Don su cika dukan abin da ya umarce su a duniya da ake zaune a ciki.

13. Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya,Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.

14. “Ka ji wannan, ya Ayuba,Tsaya ka tuna da ayyukan Allah masu banmamaki.

15. Koka san yadda Allah yakan ba su umarni,Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?

16. Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama?Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!

17. Ko ka san abin da yake sa ka jin gumiSa'ad da iskar kudu take hurowa?

18. Ka iya yin yadda ya yi,Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram,Kamar narkakken madubi?

19. Ka koya mana abin da za mu faɗa masa,Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.