Littafi Mai Tsarki

Ayu 37:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ka iya yin yadda ya yi,Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram,Kamar narkakken madubi?

19. Ka koya mana abin da za mu faɗa masa,Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.

20. A iya faɗa masa, cewa zan yi magana?Mutum ya taɓa so a haɗiye shi da rai?

21. “A yanzu dai mutane ba su iya duban haske,Sa'ad da yake haskakawa a sararin sama,Bayan da iska ta hura ta share gizagizai sarai.

22. Daga arewa wani haske kamar na zinariya ya fito mai banmamaki,Allah yana saye da ɗaukaka mai bantsoro.

23. Mai Iko Dukka, ya fi ƙarfin ganewarmu,Shi mai girma ne, da iko, da gaskiya,Da yalwataccen adalci,Ba ya garari.

24. Saboda haka mutane suke tsoronsa,Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”