Littafi Mai Tsarki

Ayu 37:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Koka san yadda Allah yakan ba su umarni,Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?

16. Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama?Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!

17. Ko ka san abin da yake sa ka jin gumiSa'ad da iskar kudu take hurowa?

18. Ka iya yin yadda ya yi,Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram,Kamar narkakken madubi?

19. Ka koya mana abin da za mu faɗa masa,Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.

20. A iya faɗa masa, cewa zan yi magana?Mutum ya taɓa so a haɗiye shi da rai?

21. “A yanzu dai mutane ba su iya duban haske,Sa'ad da yake haskakawa a sararin sama,Bayan da iska ta hura ta share gizagizai sarai.