Littafi Mai Tsarki

Ayu 37:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Saboda wannan zuciyata takan kaɗu,Kamar ta yi tsalle daga inda take.

2. Ku kasa kunne ga tsawar muryarsa,Ku saurara ga maganarsa mai ƙarfi.

3. Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka,Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.

4. Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa,Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka,Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.

5. Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce,Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.

6. Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya,Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.

7. Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,Domin dukan mutane su san aikinsa.

8. Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,Su yi zamansu a ciki.

9. Guguwa takan taso daga inda take,Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.

10. Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.

11. Yakan cika girgije mai duhu da ruwa,Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.