Littafi Mai Tsarki

Ayu 36:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ba ya rayar da masu laifi,Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.

7. Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya,Yakan kafa su har abada tare da sarakuna,A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.

8. Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi,Da kuma igiyar wahala,

9. Sa'an nan yakan sanar da su aikinsuDa laifofin da suke yi na ganganci.

10. Yakan sa su saurari koyarwa,Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta.