Littafi Mai Tsarki

Ayu 35:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Saboda yawan zalunci, jama'a sukan yi kuka,Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi.

10. Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba,Wanda yakan sa a raira waƙa da dare,

11. Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya,Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima.

12. Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba,Saboda suna da girmankan mugaye.

13. Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba,Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba.

14. “Ayuba, kai wane ne da za ka ce ba ka gan shi ba?Da kake cewa ƙararka tana gabansa,Jiransa kake yi?

15. Yanzu fa saboda bai yi hukunci da fushinsa ba,Kamar kuma bai kula da laifi ba,

16. Ayuba, maganarka marar ma'ana ce,Ka yi ta maganganu marasa hikima.”