Littafi Mai Tsarki

Ayu 34:12-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.

13. Wa ya shugabantar da shi a kan duniya?Wa ya mallakar masa da duniya duka?

14. Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,

15. Da duk mai rai ya halaka,Mutum kuma ya koma ƙura.

16. “Idan kai haziƙi ne, to, ji wannan,Kasa kunne ga abin da zan faɗa.

17. Da Allah maƙiyin adalci ne, da ya yi mallaka?Ka iya sa wa Adali, Mai Iko Dukka laifi?

18. Ka iya sa wa Allah laifi,Shi da ya ce, ‘Sarki marar amfani ne,Hakimai kuma mugaye’?

19. Ba ya nuna sonkai ga sarakuna,Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta,Gama shi ya halicce su duka.

20. Sukan mutu nan da nan,Da tsakar dare manya da ƙanana sukan shuɗe farat ɗaya,An kawar da su ba da hannun mutum ba.

21. “Gama yana ganin al'amuran mutum,Yana kuma ganin dukan manufarsa.

22. Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirinInda masu aikata mugunta za su ɓuya.

23. Ba ajiyayyen lokacin da ya ajiye wa kowane mutumDa zai je shari'a a gaban Allah.

24. Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba,Ya sa waɗansu a madadinsu.

25. Saboda sanin ayyukansu,Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,

26. Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,

27. Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗayaDaga cikin umarnansa ba.