Littafi Mai Tsarki

Ayu 34:12-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.

13. Wa ya shugabantar da shi a kan duniya?Wa ya mallakar masa da duniya duka?

14. Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,

15. Da duk mai rai ya halaka,Mutum kuma ya koma ƙura.

16. “Idan kai haziƙi ne, to, ji wannan,Kasa kunne ga abin da zan faɗa.

17. Da Allah maƙiyin adalci ne, da ya yi mallaka?Ka iya sa wa Adali, Mai Iko Dukka laifi?

18. Ka iya sa wa Allah laifi,Shi da ya ce, ‘Sarki marar amfani ne,Hakimai kuma mugaye’?

19. Ba ya nuna sonkai ga sarakuna,Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta,Gama shi ya halicce su duka.