Littafi Mai Tsarki

Ayu 33:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.

10. Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,

11. Ya saka ka a turu,Yana duban dukan al'amuranka.

12. “Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa,Gama Allah ya fi kowane mutum girma.

13. Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni,Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?

14. Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne,I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.

15. Yakan sanar a mafarkai ko a wahayiSa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su,A sa'ad da suke barci a gadajensu.