Littafi Mai Tsarki

Ayu 33:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. “Ka amsa mini, in ka iya,Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.

6. Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.

7. Don haka kada ka razana saboda ni,Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.

8. “Hakika na ji maganar da ka yi,Na kuwa ji amon maganganunka,

9. Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.