Littafi Mai Tsarki

Ayu 31:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Idan dai na kauce daga hanya,Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,

8. To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,Bari a tumɓuke amfanin gonata.

9. “Idan na yi sha'awar wata mace,Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

10. To, bari matata ta yi wa wani abinci,Bari waɗansu su kwana da ita.

11. Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,Wanda alƙalai ne za su hukunta.

12. Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

13. “Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba,Sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,