Littafi Mai Tsarki

Ayu 31:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. “Idan ina tafiya da rashin gaskiya,Ina hanzari don in aikata yaudara,

6. Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai,Zai kuwa san mutuncina.

7. Idan dai na kauce daga hanya,Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,

8. To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,Bari a tumɓuke amfanin gonata.

9. “Idan na yi sha'awar wata mace,Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

10. To, bari matata ta yi wa wani abinci,Bari waɗansu su kwana da ita.

11. Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,Wanda alƙalai ne za su hukunta.

12. Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

13. “Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba,Sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,

14. To, wace amsa zan ba Allah sa'ad da ya tashi don ya hukuntar?Me zan iya faɗa sa'ad da Allah ya zo yi mini shari'a?

15. Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa,Ba shi ne ya halicce su ba?Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa?