Littafi Mai Tsarki

Ayu 31:34-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama'a,Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni,

35. Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni,Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa,Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini.“Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,

36. Hakika da sai in ɗauke ta a kafaɗata,In kuwa naɗa ta a kaina kamar rawani.

37. Da na ba Allah dukan lissafin abin da na taɓa yi,In tinƙare shi kamar ni basarauce ne.

38. “Idan ƙasata tana kuka da ni,Ita da kunyoyinta,

39. Ko na ci amfaninta ban biya ba,Ko na yi sanadin mutuwar mai ita,

40. Ka sa ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama,Tsire-tsire marasa amfani kuma maimakon sha'ir.”Maganar Ayuba ta ƙare.