Littafi Mai Tsarki

Ayu 31:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

13. “Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba,Sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,

14. To, wace amsa zan ba Allah sa'ad da ya tashi don ya hukuntar?Me zan iya faɗa sa'ad da Allah ya zo yi mini shari'a?

15. Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa,Ba shi ne ya halicce su ba?Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa?

16. “Ban taɓa ƙin taimakon matalauta ba,Ban kuma taɓa sa gwauruwar da mijinta ya mutu ta yi kuka ba,

17. Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,

18. Tun suna yara nake goyonsu,Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.

19. “Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura,Ko wani matalauci marar abin rufa,

20. Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba,Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,

21. Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya,Don na ga ina da kafar kuɓuta,

22. To, ka sa kafaɗuna su ɓaɓɓalle daga inda suke.Ka kakkarya gwiwoyin hannuna.

23. Gama bala'i daga wurin Allah ya razanar da ni,Saboda ɗaukakarsa ba zan iya yin kome ba.

24. “Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,

25. Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,Ko saboda abin da na mallaka ne,

26. Idan ga hasken rana nake zuba ido,Ko ga hasken farin wata ne,