Littafi Mai Tsarki

Ayu 3:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.

6. Ka shafe wannan dare daga cikin shekara,Kada kuma a ƙara lasafta shi.

7. Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.

8. Ka faɗa wa masu sihiri su la'anci wannan rana,Su waɗanda suke umartar dodon ruwa.

9. Ka hana gamzaki haskakawa,Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari,

10. Ka la'anci daren nan da aka haife ni,Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala.

11. “Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata,Ko kuwa da haihuwata in mutu.

12. Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta,Ta shayar da ni kuma da mamanta?

13. Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,

14. Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulkiWaɗanda suka sāke gina fādodi na dā,

15. Da ina ta sharar barcina kamar shugabanniWaɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,

16. In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.

17. Mugaye za su daina muguntarsu a kabari,Ma'aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,