Littafi Mai Tsarki

Ayu 29:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. A sa'ad da nakan tafi kofar birni,In shirya wurin zamana a dandali,

8. Da samari sun gan ni, sai su kawar da jiki,Tsofaffi kuma su miƙe tsaye,

9. Sarakuna sun yi shiru sun kame bakinsu.

10. Manyan mutane sukan yi shiru, harshensu ya liƙe a dasashi.

11. Waɗanda suka ji labarina sukan sa mini albarka,Waɗanda suka gan ni sukan yi na'am da ni.

12. Domin sa'ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu,Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.

13. Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka,Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu,Su raira waƙa don murna.

14. Adalci shi ne suturata,Gaskiya ita ce rigata da rawanina.

15. Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.