Littafi Mai Tsarki

Ayu 29:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka,Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu,Su raira waƙa don murna.

14. Adalci shi ne suturata,Gaskiya ita ce rigata da rawanina.

15. Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.

16. Ni mahaifi ne ga matalauta,Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.

17. Nakan karya muƙamuƙin marar adalci,In sa yă saki ganimar da yă kama.

18. “Da na zaci zan mutu cikin sutura,Kwanakina kuma su riɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,

19. Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa,Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana .

20. Darajata garau take a gare ni,Bakana kullum sabo yake a hannuna.

21. Mutane sukan kasa kunne su jira, su yi shiruSa'ad da nake ba da shawara.

22. Bayan na gama magana ba wanda zai ƙara wata magana.Maganata takan shige su.

23. Suna jirana kamar yadda ake jiran ruwan sama,Da baki buɗe, kamar yadda ake jiran ruwan bazara.

24. Nakan yi musu murmushi sa'ad da suka fid da zuciya,Ba su yi watsi da fara'ata ba.

25. Nakan zaɓar musu hanyar da za su bi,Ina zaune kamar sarki a tsakanin mayaƙansu,Kamar mai ta'azantar da masu makoki.”