Littafi Mai Tsarki

Ayu 29:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya ci gaba da magana.

2. Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne,Lokacin da Allah yake lura da ni,

3. Sa'ad da fitilarsa take haskaka mini,Ta wurin haskensa kuma nake tafiya da duhu,

4. Kwanakin da nake gaɓar raina,Lokacin da ni'imar Allah take kan gidana,

5. Sa'ad da Mai Iko Dukka yake tare da ni,'Ya'yana duka kuma suka kewaye ni,

6. Sa'ad da aka wanke ƙafafuna da madara,Duwatsu kama suna ɓulɓulo mini da rafuffukan mai!

7. A sa'ad da nakan tafi kofar birni,In shirya wurin zamana a dandali,

8. Da samari sun gan ni, sai su kawar da jiki,Tsofaffi kuma su miƙe tsaye,

9. Sarakuna sun yi shiru sun kame bakinsu.

10. Manyan mutane sukan yi shiru, harshensu ya liƙe a dasashi.