Littafi Mai Tsarki

Ayu 28:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Amma ina, a ina za a iya samun hikima?A ina za a samo haziƙanci?

13. Mutane ba su san darajar hikima ba,Ba a samunta a ƙasar masu rai.

14. Zurfafa sun ce, ‘Ba ta a cikinmu,’Tekuna kuma sun ce, ‘Ba ta tare da mu.’

15. Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba.Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.

16. Ko zinariyar Ofir, ko onis,Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.

17. Ba daidai take da zinariya ko madubi ba,Ba za a iya musayarta da kayayyakin da aka yi da zinariya tsantsa ba.

18. Kada ma a ko ambaci murjani,Da duwatsu masu walƙiya.Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.

19. Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba.Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.

20. “To, daga ina hikima ta fito?A wane wuri kuma haziƙanci yake?

21. Ba talikin da ya iya ganinta,Ko tsuntsun da yake tashi sama.

22. Halaka da Mutuwa sun ce,‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishin-ƙishin a kanta.’

23. “Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta,Ya san inda hikima take,

24. Saboda yana ganin duniya ɗungum,Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.

25. Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura,Ya yi wa tekuna iyaka.