Littafi Mai Tsarki

Ayu 28:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sukan haƙa magudanar ruwa cikin duwatsu,Idanunsu sukan ga kowane abu mai daraja.

11. Sukan datse rafuffuka su hana su gudu,Su binciko abin da yake ɓoye, ya fito sarari.

12. Amma ina, a ina za a iya samun hikima?A ina za a samo haziƙanci?

13. Mutane ba su san darajar hikima ba,Ba a samunta a ƙasar masu rai.

14. Zurfafa sun ce, ‘Ba ta a cikinmu,’Tekuna kuma sun ce, ‘Ba ta tare da mu.’

15. Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba.Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.

16. Ko zinariyar Ofir, ko onis,Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.

17. Ba daidai take da zinariya ko madubi ba,Ba za a iya musayarta da kayayyakin da aka yi da zinariya tsantsa ba.

18. Kada ma a ko ambaci murjani,Da duwatsu masu walƙiya.Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.

19. Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba.Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.

20. “To, daga ina hikima ta fito?A wane wuri kuma haziƙanci yake?

21. Ba talikin da ya iya ganinta,Ko tsuntsun da yake tashi sama.