Littafi Mai Tsarki

Ayu 26:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya shata da'ira a kan fuskar teku,A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.

11. Ginshiƙan samaniya sun girgiza,Sun firgita saboda tsautawarsa.

12. Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku,Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab.

13. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau,Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu.

14. Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al'amuransa.Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa.Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?”