Littafi Mai Tsarki

Ayu 23:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa.

2. “Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni,In dinga yin nishi.

3. Da ma na san inda zan same shi,In kuma san yadda zan kai wurinsa,

4. Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.

5. Ina so in san irin amsar da zai mayar mini,Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.

6. Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni?A'a, zai saurara in na yi magana.

7. Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina,Zai tabbatar da amincina duka.

8. “Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba,Ban kuwa same shi a baya ba sa'ad da na neme shi.

9. Allah ya tafi wurin aiki a dama,Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.