Littafi Mai Tsarki

Ayu 22:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Akwai wani mutum, ko mafi hikima,Wanda zai amfani Allah?

3. Gaskiyar da kake yi za ta amfani Allah?Ko kuwa abin kirki da kake yi zai taimake shi?

4. Ai, ba don tsoron Allah da kake yi ba ne,Ya sa wannan tsautawa da jarrabawa suka same ka.

5. Ko kusa ba haka ba ne,Amma saboda zunubi mai yawa da ka yi ne.Saboda kuma dukan muguntar da ka aikata.

6. Don ka sa ɗan'uwanka ya biya ka bashin da kake binsa,Ka ƙwace tufafinsa, ka bar shi huntu.

7. Ka hana wa waɗanda suke ji ƙishi ruwan sha,Ka hana waɗanda suke jin yunwa abinci.

8. Ka mori ikonka da matsayinka,Don ka mallaki dukan ƙasar.

9. Ba ƙin taimako kaɗai ka yi ba,Amma har marayu ma ka yi musu ƙwace, ka wulakanta su.