Littafi Mai Tsarki

Ayu 21:23-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,Suna cikin farin ciki da jin daɗi,

24. Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.

25. Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba.Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.

26. Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne,Tsutsotsi su lulluɓe su duka.

27. “Na san irin tunaninku na hassada,

28. Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu,Wato mutumin da yake aikata mugunta?’

29. “Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba?Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba?

30. A ranar da Allah ya yi fushi, ya yi hukunci,A kullum mugun ne kaɗai yakan kuɓuta.

31. Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun,Ko ya mayar masa da martani.

32. Sa'ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi,A inda ake tsaron kabarinsa,

33. Dubban mutane sukan tafi wurin jana'izarsa,Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.

34. “Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta'azantar da ni da maganganun banza.Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”