Littafi Mai Tsarki

Ayu 20:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.

6. Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.

7. Amma zai shuɗe kamar ƙura.Waɗanda dā suka san shi,Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.

8. Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.

9. Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.

10. Tilas 'ya'yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.