Littafi Mai Tsarki

Ayu 20:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. A lokacin da yake gaɓar samunsa,Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.

23. Bari ya ci duk irin abin da yake so!Allah zai hukunta shi da hasala da fushi.

24. Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe,Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.

25. Kibiya za ta kafe a jikinsaTsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini,Razana ta kama zuciyarsa.

26. Aka hallaka dukan abin da ya tattara,Wutar da ba hannun mutum ya kunna baTa ƙone shi, shi da iyalinsa duka.

27. Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum,Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.

28. Dukan dukiyarsa za a hallaka ta a rigyawar fushin Allah.

29. “Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,Wadda Allah ya ƙayyade musu.”