Littafi Mai Tsarki

Ayu 19:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Allah ya zaburo mini da fushi,Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.

12. Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini,Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.

13. “'Yan'uwana sun yashe ni,Na zama baƙo ga idon sanina.

14. Dangina da abokaina sun tafi.