Littafi Mai Tsarki

Ayu 18:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bildad ya amsa.

2. “Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru?Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.

3. Me ya sa kake tsammani mu dakikai ne kamar shanu?

4. Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji.Duniya za ta ƙare ne sabili da kai?Za a kawar da duwatsu sabili da kai?

5. “Za a kashe hasken mugun mutum,Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.

6. Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.

7. A dā gagau yake tafiya, amma yanzu ɗingishi yake yi,Shawararsa ta kāshe shi.

8. Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko.Tarkon ya kama ƙafafunsa.