Littafi Mai Tsarki

Ayu 15:32-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Kafin kwanakinsa su cika zai bushe,Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.

33. Zai ama kamar itacen inabiWanda 'ya'yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna,Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin 'ya'ya ba.

34. Marasa tsoron Allah ba za su sami zuriya ba,Wuta za ta cinye gidajen da aka gina da dukiyar rashawa.

35. Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta.Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”