Littafi Mai Tsarki

Ayu 13:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?Kuna goyon bayan Allah?Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?

9. Da Allah ya bincike ku sosai,Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?

10. Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,Duk da haka zai tsauta muku,

11. Ikonsa kuwa zai razana ku.

12. Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.

13. “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.Duk abin da zai faru, ya faru.

14. A shirye nake in yi kasai da raina.

15. Na fid da zuciya ɗungum.To, in Allah ya kashe ni, sai me?Zan faɗa masa ƙarata.