Littafi Mai Tsarki

Ayu 13:23-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Kuskure da laifi guda nawa na yi?Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?

24. Me ya sa kake guduna?Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?

25. Ƙoƙari kake ka firgita ni?Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai,Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai.

26. Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina,Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.

27. Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi,Kakan lura da kowace takawata,Har kana bin diddigin sawayena.

28. Saboda wannan na zama abin kallo,ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.”