Littafi Mai Tsarki

Ayu 13:1-2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1-2. “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa,Na gane da shi sarai.Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani.Ba ku fi ni da kome ba.

3. Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba,Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.

4. Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi.Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.

5. Kada ku faɗi kome,Wani sai ya ce kuna da hikima!

6. “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.

7. Me ya sa kuke yin ƙarya?Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?

8. Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?Kuna goyon bayan Allah?Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?

9. Da Allah ya bincike ku sosai,Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?