Littafi Mai Tsarki

Ayu 13:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.

13. “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.Duk abin da zai faru, ya faru.

14. A shirye nake in yi kasai da raina.

15. Na fid da zuciya ɗungum.To, in Allah ya kashe ni, sai me?Zan faɗa masa ƙarata.

16. Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni,Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.

17. Sai a saurari bayanin da zan yi.

18. A shirye nake in faɗi ƙarata,Domin na sani ina da gaskiya.

19. “Ya Allah, za ka yi ƙarata?Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.

20. Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo,Ka yarda da su, sa'an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba.

21. Wato ka daina hukuncin da kake yi mini,Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.

22. “Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa.Ko kuma ka bari in yi magana, sa'an nan ka amsa mini.

23. Kuskure da laifi guda nawa na yi?Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?