Littafi Mai Tsarki

Ayu 12:6-12-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma ɓarayi da marasa tsoronAllah suna zaune cikin salama,Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.

7. “Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,Suna da abu mai yawa da za su koya maka.

8. Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.

9. Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.

10. Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.

11. Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.

12-13. “Tsofaffi suna da hikima,Amma Allah yana da hikima da iko.Tsofaffi suna da tsinkaya,Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.