Littafi Mai Tsarki

Ayu 11:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Idan dakikan mutane sa yi hikima,To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13. “Ayuba, ka shirya zuciyarka,Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14. Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15. Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,Da ƙarfi da rashin tsoro.

16. Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

17. Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.Kwanakin ranka mafiya duhuZa su yi haske kamar ketowar alfijir.

18. Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.

19. Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba,Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.

20. Amma mugaye za su dudduba ko'ina da fid da zuciya,Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta.Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”