Littafi Mai Tsarki

Ayu 10:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna,Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.

13. Amma yanzu na sani,Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.

14. Jira kake ka ga ko zan yi zunubi,Don ka ƙi gafarta mini.

15. Da cewa na yi zunubi, na shiga uku ke nan a wurinka.Amma sa'ad da na yi abin kirki ba na samun yabo.Ina baƙin ciki ƙwarai, kunya ta rufe ni.

16. Da zan ci nasara a kan kowane abu,Da sai ka yi ta farautata kamar zaki,Kana aikata al'ajabai don ka cuce ni.

17. A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni,Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina,Kakan yi mini farmaki a koyaushe.

18. “Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni?Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!