Littafi Mai Tsarki

Ayu 1:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. 'Ya'yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci 'yan'uwan nan nasu mata su halarci liyafar.

5. A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.

6. Sa'ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su.