Littafi Mai Tsarki

A.m. 9:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

6. Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”

7. Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba.

8. Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.

9. Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.

10. To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na'am, ya Ubangiji.”

11. Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙiye, ka tambaya a gidan Yahuza, ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan, yana addu'a,

12. har ma a cikin wahayi ya ga wani mutum, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ya sāke samun ganin gari.”

13. Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.

14. Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu'a da sunan har a nan ma.”

15. Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma'aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al'ummai, da sarakuna, da kuma Isra'ilawa.

16. Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”