Littafi Mai Tsarki

A.m. 9:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shawulu kuwa yana kan tsananta kashedi da gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su, sai ya je wurin babban firist,

2. ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.

3. Yana tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba zato sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.

4. Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

5. Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

6. Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”

7. Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba.

8. Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.

9. Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.