Littafi Mai Tsarki

A.m. 5:26-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.

27. Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su,

28. ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”

29. Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.

30. Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume.

31. Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.

32. Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”

33. Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su.