Littafi Mai Tsarki

A.m. 28:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Su kuwa da suka tuhume ni, suna so su sake ni, don ban yi wani laifi da ya isa kisa ba.

19. Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zamar mini dole in nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar, ba don ina ƙarar jama'armu ba ne.

20. Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra'ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”

21. Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan'uwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗi wata mummunar magana game da kai.

22. Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra'ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko'ina ana kushenta.”

23. Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.